Arewaci da Kudancin Sudan sun cimma matsaya

Image caption Shirin zabe a Sudan

Kwamitin kungiyar tarayyar Afirka da Mista Thabo Mbeki ke jagoranta ya bayyana cewa Kudanci da kuma Arewacin Sudan sun amince a kan wani tsari da zai warware batutuwan da suka ki ci- suka ki- cinyewa a tsakaninsu.

Bayan shafe tsawon lokaci ana tattaunawa ciki da kuma wajen Sudan, kwamitin ya bayyana cewa Arewa da Kudancin kasar sun amince akan wadansu batutuwa.

Sun hada da cewa duk rintsi, ba za'a cigaba da yakin basasar da aka dade ana yi a kasar ba.

Sannan kuma matakan da za'a sanya a kan iyakoki zasu kasance masu sauki ta yadda makiyaya daga arewacin kasar ka iya cigaba da zuwa kiwo kudu.

Sannan an tabo batutuwan da suka shafi 'yan cin al'umma.

Sai dai wani batu da har yanzu ke da sarkakiya shi ne game da garin Abyei, wanda ke da arzikin mai.

Shima dai an amince za'a kada kuri'a ta daban a kansa wanda shugaban kasar Sudan da kuma wani babba daga bangaren kudanci ne zasu zauna su amince akan ko waye ya cancanci ya kada kuri'a a kai.

Kuri'ar raba gardamar da ake shirin jefawa, wadda ka iya baiwa kudancin Sudan 'yancin kai a watan Janairu mai zuwa dai na ta janyo fargaba.

Kuri'ar kuma ta kasance wani muhimmin mataki a yarjejeniyar zaman lafiyar da ake son cimmawa wadda za ta kawo karshen yakin basasar da aka dauki tsawon lokaci ana yi.