Yarima William zai yi aure

Yarima william da Kate
Image caption An ba da sanarwar auren Yarima William da Kate

A Birtaniya an bada sanarwar cewa, Yarima William - wanda shi ne na biyu a jerin masu jiran hawa gadon sarauta kasar- zai auri budurwarsa , Kate Middleton, a badi.

Praministan Birtaniya, David Cameron, ya bayyana auren da ake shirin yi da cewa, wata rana ce ta murna sosai ga kasar baki daya.

Ana sa ran cewa bayan bikin, ma'auratan zasu tare a yankin arewacin Wales, inda Yarima William zai ci gaba da aikinsa a rundunar mayakan saman Birtaniya, a matsayinsa na matukin jirgin helikopta.

Shi dai Yarima William ya fara neman Kate ne shekaru tara da suka gabata, inda akai musu baiko a watan Oktoba lokacin da suka je hutu kasar Kenya.