Burtaniyya za ta yi diyyar azabtar da tsararru

Image caption Binyamin Muhammad, daya daga cikin tsararrun

Gwamnatin Burtaniya za ta biya gwaggwabar diyya ga kimanin mutane goma sha biyu da aka tsare a baya bisa zargin aikata ta'addanci.

Gwamnatin dai ta amince da biyan mutane wadanda yan Burtaniya ne ko kuma mazauna kasar miliyoyin daloli a matsayin diyya domin kaucewa bayyana bayanan sirri a gaban kotu.

Wasu daga cikin wadanda za'a biya diyyar an tsare su ne a sansanonin Guantanamo Bay mallakar Amurka amma sun tuhumi hukumomin leken asiri na Burtaniya da hadin baki wurin azabtar da su a Morocco, da Pakistan da kuma wasu wuraren dabam.

Wakilin BBC ya ce sai dai duk da haka za'a saurari zargin da ake yi wa hukumomin leken asiri na Burtaniya na hada baki wurin azabatar da wadanda ake zargi da aiki ta'addanci a wata kotun bincike da aka kafa karkashin wani tsohon alkalin kotun daukaka kara.