Walda ce ta haddasa gobarar China

Image caption Yan kwana-kwana na kashe gobara

Jami'an China sun ce aikin walda ba bisa ka'ida ba shi ne ya haddasa gobarar da ta hallaka fiye da mutane hamsin a wani gidan bene da ke birnin Shanghai a ranar Litinin.

Mutane da dama kuma na kwance a asibiti sanadiyyar gobarar.

Jami'an na China sun ce an kama mutane hudu bisa zargin haddasa gobarar.

Gobarar dai ta tashi ne lokacinda ake yiwa gidan mai hawa ashirin da takwas kwaskwarima.