Alpha Conde ya yi nasara a zaben Guinea

Image caption Farfesa Alpha Conde

Hukumar zaben Guinea ta ce jagoran yan adawa Alpha Conde ne ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi da kaso hamsin da biyu na kuri'un da aka kada.

Wannan dai shi ne zaben shugaban kasa na farko a Guinea bisa turbar dimokradiyya tun bayan da kasar ta samu yancin kai a shekarar alif da dari tara da hamsin da takwas kuma ya biyo bayan mulkin soji ne na shekaru biyu.

Shugaban hukumar zaben, Siaka Toumani Sangare ne ya baiyana sakamakon bayan da aka yini cikin halin dar-dar a Conakry, babban birnin kasar inda magoya bayan abokin takarar Mr. Conde Cellou Dalein Diallo suka kona tayoyi tare da sanya shingaye bisa tituna.

Yace: Farfesa Alpha Conde na da kuri'u miliyan guda da dubu dari hudu da saba'in da hudu da dari tara da saba'in da uku, wato kaso hamsin da biyu na kuri'un da aka kada inda Alhaji Mamadou Cellou Dalein Diallo ya samu kuri'u miliyan daya da dubu dari uku da talatin da uku da dari shida da sittin da shida, wato kaso arba'in da bakwai na adadin kuri'un.