Cutar Kwalara na kara yin barna a Haiti

Wani mai fama da kwalara a Haiti
Image caption Wani mai fama da kwalara a Haiti

Ma'aikatar lafiya a Haiti ta ce, a yanzu fiye da mutane dubu ne suka mutu, sakamakon annobar cutar kwalara da ta afkawa kasar.

Fiye da mutane dubu goma sha shidda ne suka nemi magani a asibitoci, kuma annobar kwalarar ta shafi kusan kowane lardi a kasar ta Haiti.

A jiya Litinin, dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya sun bindige wasu mutane biyu, a lokacin zanga zangar da jama'a suka yi, suna zargin sojojin da kai cutar kwalarar a kasar.

Majalisar ta dage a kan cewa, ba wata shaidar da ke nuna cewa zargin gaskiya ne.