Rushewar gini ta kashe mutane sittin a India

Image caption Ginin da ya rushe a Delhi

Jami'ai a kasar India sun ce akalla mutane sittin ne suka rasu sanadiyyar rugujewar wani gini mai hawa biyar a garin Delhi da maraicen jiya.

Haka kuma wasu da dama sun samu munanan raunuka kuma duk da aikin ceton da aka kwana ana yi, kawo yanzu akwai mutanen da ba'a kai ga fito da su daga cikin rusasshen ginin ba.

Wani dan unguwar da ginin ya rushe ya shaidawa BBC cewa mutanen da abin ya rutsa da su na da yawa amma dai zuwa karfe tara da rabi na dare an fitar da yara ashirin da biyu.

Kawo yanzu dai ba'a san musabbabin rushewar ginin ba amma jami'an India na cewa ambaliyar ruwa da aka yi ta raunana harsashin ginin.