Abinci ya wadata a Nijar

Tutar jamhuriyar Nijar
Image caption Abinci ya wadata a Nijar

A jamhuriyar Nijar, yanzu haka manoman kasar na cikin wadatar abinci, sakamakon isasun albarkatun noman da suka samu a bana. Ana hasashen cewa yawan abincin da aka samu a bana, musamman ma wake, ba a taba samun irinsa ba a cikin shekaru arba'in din da suka wuce a kasar.

Ko a cikin makon da ya gabata, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa, yawan amfanin gonar da za a samu a bana a Nijar din, zai zarta na bara da kashi 60 cikin dari.

Hakan dai ya sa manoman yin kira ga gwamnatin da ta taimaka masu, ta hanyar sayen abincin da daraja daga gare su, a maimakon 'yan kasuwa su saye shi a farashin da bai taka kara ya karya ba.

Karancin ruwan saman da aka samu a daminar bara ya haddasa matsalar karancin abinci a Nijar din.