Hare-hare na hana yaki da kwalera a Haiti

Image caption Hare-hare a Haiti

Majalisar dinkin duniya ta ce hare-haren da ake kaiwa ma'aikatan agaji da ke yaki da annobar kwalera a Haiti na kawo tarnaki ga gudunmawar da kasashen duniya ke yi.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ce an soke tashin jiragen kai tallafi, an kuma dakatar da shirin tsarkake ruwa, sannan an sace tare da kona abinci ton dari biyar a wani hari da aka kai rumbun kayan agaji.

Hare-haren sun biyo bayan zargin da yan Haiti su ke yi ne cewa dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya ne suka shigar da kwayar cutar kwalera da ta kashe fiye da mutane dubu cikin kasar.

Wakiliyar BBC ta ce babban jami'in majalisar dinkin duniya a Haiti ya ce tsofaffin sojoji da masu laifuffuka ne suka shirya hare-haren da nufin hana gudanar da zabe a kasar.