Argentina ta doke Brazil

Argentina ta doke Brazil
Image caption Wannan ne karo na farko da Argentina ta doke Brazil a cikin shekaru 6

Argentina ta doke Brazil da ci daya mai ban haushi a wasan sada zumuntar da suka buga a filin wasa na Khalifa da ke kasar Qatar.

Lionel Messi ne ya zira kwallon ana gab da a kammala wasan.

Messi ya karbi kwallon ne daga wurin Ezequiel Lavezzi, sannan ya yanke mutane biyu kafin daga bisani ya makata raga daga yadi 18.

Duka bangarorin biyu dai sun kai hare-hare ta hannun Ronaldinho da Messi - inda Messi da Dani Alves duk suka yi kararrawa.

Wannan ne karo na farko da Argentina ta doke Brazil a cikin shekaru shida.

Wasu daga cikin wasannin sada zumuntar da aka buga:

Switzerland 2 - 2 Ukraine Denmark 0 - 0 Czech Republic Sweden 0 - 0 Germany Netherlands 1 - 0 Turkey Austria 1 - 2 Greece South Africa 0 - 1 United States Italy 1 - 1 Romania Ireland Republic 1 - 2 Norway Northern Ireland 1 - 1 Morocco Portugal 4 - 0 Spain