Kotun Senegal ba ta da hurumin hukunta Hissene Habre

Yaran Chadi
Image caption Yaran Chadi

Kotun kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, ta kasashen yammacin Afirka, ta hana kotun kasar Senegal yiwa tsohon shugaban Chadi, Hissene Habre shari'a.

Kotun ta CEDEAO ta bada umarnin a kafa wata kotu ta musamman a karkashin kungiyar Tarayyar Afirka, wadda zata yiwa tsohon shugaban kasar Chadin shari'a.

Ana zargin Hissene Habre da aikata laifufukan yaki da kuma keta hakkin bil'adama, a lokacin da yake mulki tsakanin 1982 zuwa 1990.