Kotun laifukan yaki za ta yi bincike a Najeriya

Moreno Ocampo
Image caption Ocampo yana ganin bai kamata masu laifi su sha ba

Jama'a na cigaba da maida martini ga matakin da kotun hukunta Manayn Laifiuka ta ta kasa da kasa ta ce za ta dauka da nufin gudanar da bincike gama da rikicin jihar Filato.

Mai gabatar da kara na kotun hukuntalaifuka kan bil'adama, Louis Mareno Okampor, ya ce suna kan nazarin rikicin da zimmar kaddamar da bincike domin gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a ciki.

Jihar Filato dai ta sha fama da rikice-rikice na kabilanci da addini wadanda kuma kan janyo hasarar dimbin rayuka da dukiyoyi, kuma hukumomi a Nijeriyar sun sha kafa kwamitocin bincike amma kawo yanzu babu wanda aka hukunta sabo da hannu a ciki.

Masu shigar da kara a kotun hukumta manyan laifuifuka ta duniya, ICC ta kaddamar da binciken share fage a Nijeriya da Honduras, don tantance ko an aikata laifufukan yaki da na cin zarafin BilAdama a wadannan kasashe.

Babban mai shigar da kara na kotun ta Kotun Laifukan Yaki ta Duniya, Luis Moreno Ocampo ya ce kotun ta fara bincike dangane da juyin mulkin da aka yi bara a Honduras, bayan da ta samu rahotannin dake cewa akwai yiwuwar an keta hakkin BilAdama a kasar.

Sai kuma Mr Ocampo ya ki ya yi bayani kan binciken da kotun ta ICC ta fara a Nijeria.

Wasu rahotanni na cewa binciken zai maida hankali ne a kan rikicin kabilanci da na addini da aka yi a jihar Pilato dake tsakiyar Nijeria.