Boko Haram ta harbe mutane a Maiduguri

'Yan sanda a Nijeriya sun ce an kashe mutane biyu a wani hari da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai shi, a wani masallaci a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce an kuma raunata wani karamin yaro, a lokacin da 'yan bindigar su biyu suka isa masallacin, lokacin sallar Juma'a, suka bude wuta kan masallata.

Kakakin 'yan sandan ya ce an kama mutane sha uku, ciki har da wadanda ake zargi da kai harin.

Ya ce mutanen 'yan kungiyar Boko Haram ce, ta 'yan kishin addinin da ake zargin suna kashe masu unguwani da kuma 'yan sanda a arewa maso gabashin Nijeriya.