EFCC za ta binciki Amos Adamu

Amos Adamu
Bayanan hoto,

Amos Adamu ya yi watsi da zargin cin hancin

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, EFCC, za ta binciki Dr Amos Adamu bayanda hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta same shi da yunkurin karbar cin hanci.

EFCC ta ce za ta karbi rahoton da FIFA ta fitar kan batun, kuma idan har ta samu Adamu da laifi, ba za ta yi wata-wata ba wajen gurfanar da shi gaban kuliya.

Sai dai hukumar ta EFCC ta kara da cewa, za ta shaida wa duniya sakamakon binciken da ta gudanar idan ta gano Amos bai aikata wani laifi ba.

Kakakin hukumar EFCC Femi Babafemi ya shaida wa BBC cewa: "Ba zamu yi wasa da batun ba, don haka ne ma za mu yi bincike da zummar gano gaskiyar zargin. Kuma zamu gani ko hakan ya shafi dokokin kasarmu, gabanin mu dauki mataki na gaba".

Hukumar ta ce a wurinta, yunkurin karbar cin hancin ya isa ta gurfanar da Amos Adamu a gaban kuliya, sai dai ta kara da cewa, idan bata same shi da laifi ba, to lallai za ta shaida wa duniya.

A ranar Alhamis ne kwamitin da'a na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ya dakatar da Amos Adamu daga harkokin kwallo har tsawon shekaru uku, sannan ya ci tarar sa dala 10,000.

Hukumar ta kuma dakatar da Reynald Temarii na kasar Tahiti, wanda shi ma mamba ne a kwamitin zartarwarta tsawon shekara guda, tare da tarar dala 5,000.

Kwamitinta na da'a na FIFA ya same su da laifin yunkuri sayar da kuri'unsu a zaben kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarun 2018 da 2022.

'Zan daukaka kara'

Sai dai jim kadan bayan yanke hukuncin, Amos Adamu ya fitar da sanarwa inda ya yi watsi da hukuncin.

Ya ce: "ban ji dadin wannan hukunci da kwamitin da'ar ya yanke ba, na yi imanin cewa za a wanke ni daga zargin,".

"Nan ba da jimawa ba zan daukaka kara game da hukuncin da suka yanke."

Tsofaffin mambobin kwamitin zartarwar hudu - Slim Aloulou na Tunisia da Amadu Diakite na Mali da Ahongalu Fusimalohi na Tonga da Ismael Bhamjee na kasar Botswana - duk sun fuskanci hukunci daga FIFA.

An dakatar da Bhamjee shekaru hudu, Diakite da Fusimalohi shekaru uku-uku, Aloulou shekaru biyu, sannan dukkansu a ka ci tararsu dala 10,000.

Rahoton Sunday Times

A watan Oktoba ne Jaridar Sunday Times, ta wallafa cewar Mr Amos Adamu, wanda ya fito daga Nigeria da kuma Reynold Temarii dan Kasar Tahiti, dukkaninsu sun nuna a shirye su ke su sayar da kuri'un su na zabar kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarun 2018 da 2022.

Jaridar ta ce, Mr Adamu ya bukaci a bashi dala dubu dari takwas don ya gina filayen wasa a Najeriya, da aka tambaye shi yana gani idan a ka bashi kudi don gudanar da aikin kashin kansa hakan za ta sa ya sauya yadda zai kada kuri'a, sai ya ce, ''lallai hakan zai yi tasiri.Tabbas kuwa''.

Ya shaida wa 'yan jaridar cewa shi za a baiwa kudin, ba gwamnatin kasarsa ba.

Ya kara da cewa, yana neman hanyar da zai samu kudi kimanin fan dari biyar don gina filayen wasa.

Jaridar ta ce shi ma Reynald Temarii, wanda shi ne shugaban wata gamammiyar kungiyar kwallon kafa ta yankin Oceania, ya tattauna batun biyan sa kudi don gina wata makarantar koyar da wasanni.