Sarakunan Ghana sun bukaci a ba su kudin mai

Shugaba John Atta Mills na Ghana
Image caption Shugaba John Atta Mills na Ghana

Sarakunan gargajiya a yammacin kasar Ghana, inda ake sa ran fara hakar man fetur a wata mai zuwa, sun nemi a yi amfani da kashi goma cikin dari na harajin man da za a samu wajen bunkasa yankin.

Sarakunan gargajiyan sun ce suna bukatar a kashe kudaden ne a yankunansu don kaucewa irin matsalolin da ake fama da su a yankin Naija Delta na Najeriya.

A yankin na Naija Delta dai 'yan bindiga na fafutikar neman karin wani kaso na kudaden da ake samu a albarkatun man fetur.

Ministan kudi na kasar ta Ghana, Kwabena Duffuor, ya ce bunkasa tattalin arzikin kasar ba tare da an kara gibin da ke tsakanin masu hali da matalauta ba babban kalubale ne.