Tarnakin biyan sabon albashi a Nijeriya

Yajin ma'aikata na sa tituna su koma kamar an share a Nijeriya
Image caption Yajin ma'aikata na sa tituna su koma kamar an share a Nijeriya

A kwanakin baya ne kungiyar kwadago ta Nijeriya ta shiga yajin aiki na gargadi, bayan da aka kasa cimma daidaito tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayyar kasar bisa karin albashi.

Kungiyar kwadagon dai na son samun naira dubu goma sha takwas ne a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar.

To amma yajin aikin bai kawo biyan bukata ba.

Ma'aikata dai sun sha yin irin wannan yajin aiki domin neman karin albashi, sai dai kuma watanni ko 'yan shekaru bayan karin albashin sai kaga an koma gidan jiya.

Domin tattaunawa kan wannan batu a filinmu na Ra'ayi Riga, mun gayyato bakin da suka hada da; Comrade Danjuma Papakunene, na kungiyar kwadago ta Nijeriya, da Malam Sani Ya'u Babura, mai sharhi kan harkokin yau da kullum, kuma tsohon shugaban yankin arewa maso yammacin Nigeria na kungiyar dillalan mai ta kasa, wato IPMAN, da kuma , Senata Hassan Muhammad Nasiha, mataimakin shugaban kwamitin kwadago da samar da ayyukan yi a majalissar dattawan Nijeriya.