An fara taron koli na kungiyar NATO

Babban taron NATO a Lisbon
Image caption Babban taron NATO a Lisbon

Shugabannin kasashen kungiyar NATO sun fara taron koli a birnin Lisbon na kasar Portugal, don duba yadda za su fuskanci barazanar tsaro da ka iya tasowa.

Ana sa ran mambobin kungiyar za su amince da wani sabon kawance ta fuskar soji wanda ake sa ran zai sauya fasalin rundunar tsaro ta NATO nan da wadansu shekaru masu zuwa.

Taron kolin zai kuma duba dabarun janye dakarun kungiyar daga Afghanistan.

Tun bayan da aka kawo karshen yakin cacar baka ne dai kungiyar ta NATO ke kokarin samun bakin fada-a-ji.

Don haka ne ta sauya manufofinta da tsare-tsarenta ta yadda za su dace da yanayin tsaron da duniya ke fuskanta.

Babban sakataren kungiyar, Anders Fogh Rasmussen, ya kwatanta sabuwar NATO wadda ake sa ran samrawa da na'urar kwamfuta ta zamani mai saurin gaske.

Za kuma a yi kokarin cimma matsaya a kan matakan da ya kamata a dauka a Afghanistan yayinda aka ayyana shekara ta 2014 a matsayin lokacin da kungiyar ta NATO za ta danka al'amuran tsaro ga dakarun kasar.

Sai dai a zahirance kungiyar ta NATO za ta ci gaba da taka rawa wajen horar da dakarun Afghanistan; hasali ma, babu ko tantama samar da rundunar tsaro mai tasiri a Afghanistan ce dabarar janyewar dakarun kungiyar daga kasar.