Baraka a kungiyar CAN a kan karba-karba

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Wata dambarwa ta kunno kai a kungiyar mabiya addinin kirista ta Najeriya, wato CAN, shiyyar arewacin kasar.

Yanzu haka dai ana fama da takaddama tsakanin wadansu 'yan kungiyar da ke goyon bayan tsarin karba karbar mulki tsakanin kudanci da arewacin Najeriyar, da kuma wadanda ke da wani ra'ayi na dabam.

Kungiyar dai ta fada cikin wannan rikici ne tun bayan da kwamitin tantance masu neman takara a jam'iyyar PDP daga arewacin Najeriyar ya ziyarci Kaduna, inda wadansu 'yan kungiyar ta CAN da suka gana da kwamitin suka nuna goyon baya ga fitar da dan takarar shugabancin kasar daga arewa, to amma daga baya wadansu 'yan kungiyar suka tsame kansu daga matsayin.

A yanzu dai wadansu 'yan kungiyar ta CAN masu goyon bayan karba-karba sun kafa wata kungiya mai suna Northern Christian Leaders Eagle Eye Forum don ganin mulki ya koma arewacin kasar a shekarar 2011.

Pastor Aminci Habu shi ne shugaban kungiyar, ya kuma shaidawa BBC cewa sun kirkiri ne saboda ganin cewa “ya kamata…a bi gaskiya, a tsaya kan gaskiyan nan; saboda wannan mulki shekara hudun nan, idan ta zo, an gama arewa, sai mu koma can kudu wajen Ibo a dubi Kirista dan uwanmu a bas hi; ka ga mun zauna lafiya ke nan”.

Sai dai Reverend John Joseph Hayab, wanda kusa ne a kungiyar ta CAN, ya ce ba da yawunsu Pastor Aminci Habu ya yi magana ba.

“Idan Pastor Aminci ya wakilci CAN [to] mai yiwuwa akwai wata CAN daban wadda ban saniba; mai yiwuwa ta shi CAN din daban da tawa...”, inji Reverend Hayab.