An samu jinkiri a aikin ceto a New Zealand

Mahakar ma'adinai a New Zealand
Image caption Mahakar ma'adinai a New Zealand

A kasar New Zealand, masu aikin ceto na ci gaba da fuskantar jinkiri saboda damuwar da ake nunawa ta yiwuwar shakar iska mai guba a wata mahakar ma'adinai, inda wani abu ya fashe ya kuma rutsa da masu hakar ma’adinai.

Rahotanni na baya-bayan nan daga Kogin Pike—inda mahakar ta ke—na nuna cewa ma'aikatan agaji sun kwashe sa'o'i ashirin suna jira a ba su damar shiga mahakar ma'adinan.

'Yansanda sun ce suna jiran sakamakon gwaje-gwajen iskar da aka gudanar don tabbatar da cewa babu iska mai guba a mahakar ma'adinan.

Ya kamata a ce ya zuwa yanzu dai an kaddamar da aikin ceton amma 'yan sandan sun ce jinkirin ya zama wajibi.

A halin da ake ciki kuma, 'yan sandan sun tabbatar da cewa akwai 'yan Burtaniya da 'yan Australiya a cikin masu hakar ma'adinai ashirin da tara da ba a gansu ba tun bayan hadarin.

Kafofin yada labarai na kasar sun bayar da rahoton cewa hudu daga cikin masu hakar ma'adinan na amfani ne da fasfon kasar Burtaniya.

Tun bayan fashewar dai ba a sake jin duriyar mutanen ba.