Wani kusa a gwamnatin Obama yace Koriya ta Arewa ta yi tsaurin ido

Wani kusa a gwamnatin Obama ya ce bayanai na baya-baya da Koriya ta Arewa ta yi kan shirin nukiliyarta, karin matakai ne dake nuna tsaurin ido.

Jami'in, wanda yayi magana da manema labarai, bisa sharadin cewa ba zasu bayyana sunansa ba, ya ce ikirarin da Koriya ta Arewa ta yi na gina wata sabuwar tashar inganta karfen uranium, sun saba wa alkawarin da ta dauka, da kuma yarjejeniyar da aka yi da ita.

Furucin ya biyo bayan labarin da wani masanin kimiyar Amurka, Siegfried Hecker ya bayar ne cewa lokacin da ya ziyarci tashoshin nukiliyar koriya ta arewan, an nuna masa daruruwan na'urorin da suka ce suna amfani da su wajen inganta Uranium don samun makamashin nukiliya.