An kashe mutane ashirin a Somalia

Somalia
Image caption Somalia

Mutane kimanin ashirin ne aka kashe cikin kwanaki biyu da aka kwashe ana tashin hankali a yankin tsakiyar kasar Somalia, tsakanin kungiyar dakarun sa kai ta Ahlu Sunna wal Jama'a, da kuma kungiyar masu tayar-da-kayar-baya ta Al-Shabaab.

Mutane da dama sun tsere daga gidajensu saboda fadan, kuma rahotanni na cewa dukkan bangarorin na kai karin dakaru.

Fadan ya faro ne bayan da mayakan kungiyar Ahlu Sunnah suka kai farmaki a kan wani sansani na al-Shabaab, dake kusa da garin Guri-Eel, a lardin Galguduud.