An zabi Atiku a matsayin dan takarar Arewa

Image caption Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar

A Najeriya, Kwamitin dattawan arewa sun tsaida tsohon mataimakin shugaban kasa, a matsayin dankarar da zai wakilici arewacin kasar domin fafatawa da shugaba Goodluck Jonathan a zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP.

Kwamitin dai ya zabo Atiku ne , bisa tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Aliyu Gusau da kuma gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki.

Kwamitin wanda Mallam Adamu Ciroma ke jagoranta, ya nemi daukacin 'yan Najeriya da su bawa Atiku goyon bayansu ganin cewa, Jam'iyyar PDP mai mulki ta mika tsarin karba-karbar da ta ke yi ne ga yankin arewa.

Da yake bayyana matakin da kwamitin ya dauka ga manema labarai, Alhaji Abdulkadir Sabo Bello, wanda shi ne sakataren kwamitin dattawan.

Ya ce batun tabbatar da bin tsarin karba-karba a jam'iyyar PDP ne ya sanya kwamitin zagayawa da kuma tattaunawa da shugabanni daban-daban a fadin kasar.

Inda kuma a karshe suka zabi Alhaji Atiku Abubakar, domin kasancewa dantakara daya tilo da zai wakilci yankin a zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP.

'Duka Arewacin Najeriya a ke yi wa'

Alhaji Abdulkadir Sabo Bello ya kuma shaida wa BBC cewa sai da suka samu tabbacin hadin kai daga sauran 'yan takarkarun kafin su kai ga yanke wannan hukunci.

Major Bilya wanda shi ne jagoran yakin neman zaben Janar Aliyu Gusau a jihar Kaduna, ya shaida wakilin BBC Naziru Mika'il ta wayar tarho cewa, su ba sa fushi da ikon Allah:

"Idan ka duba za ka ga cewa duka da Atiku da Aliyu Gusau babu wani banbanci, domin sun dade suna tare, kuma duka Arewacin Najeriya a ke yi wa".

Tun da farko dai dukkan 'yan takarkarun sun bayyana cewa za su amince da dukkan matakin da kwamitin ya dauka.

Masu lura da al'amura dai na ganin matakin da kwamitin dattawan Arewan ya dauka zai zafafa fafutukar da ake yi a jam'iyyar ta PDP.

Ganin cewa a yanzu kalubale zai rage ne tsakanin shugaba Goodluck Jonathan, wanda shi kadai ne ya bayyana sha'awarsa ta neman shugabancin kasar daga yankin Kudu a PDPn, da kuma Atiku Abubakar wanda yanzu zai zamo daya tilo daga Arewa.

Abin jira a gani dai shi ne ko matakin da 'yan takarkarun suka dauka na marawa daya baya, zai cika burin da suke da shi na ganin mulkin kasar ya komo yankin Arewa.