Daruruwan mutane sun hallaka a turmutsitsi a Cambodia

Turmutsitsi a Cambodia
Image caption Turmutsitsi a Cambodia

A kalla mutane 330 sun hallaka a Cambodia, a wani turmutsitsin da aka yi a lokacin wani biki, a Phnom Penh, babban birnin kasar.

Rahotannin sun ce wasu daruruwan mutane kuma sun jikata. Dimbin jama'a ne suka taru a wani karamin tsibiri da ke kusa da birnin na Phnom Penh, domin halartar bikin ranar ruwa na shekara shekara.

Wani da ya ganewa idanunsa abinda ya faru yace, an samu rudani ne, a lokacin da mutanen da aka tattake suka fadi a some.

Ganin haka ya sa mutanan dake daya bangaren suka ruga wajen wata gada da ta hada tsibirin da sauran garin.

An tattake wasu mahalarta bikin, yayin da wasu kuma suka fado daga kan gadar.