Ministan shari'a na Japan ya ajiye aikinsa

Mista Minoru Yanagida
Image caption Mista Minoru Yanagida, tsohon ministan shari'a na Japan

Ministan Shari'a na kasar Japan ya ajiye aikinsa bayan ya jawo wata takaddama.

Da wasa ne dai Minoru Yanagida ya furta wasu kalamai yayin da ya ke jawabi ga magoya bayansa; to amma sai allura ta tono masa garma, don kuwa an tilasta masa ajiye aikinsa.

Mista Yanagida cewa ya yi aikinsa na minista na da sauki saboda wadansu kalmomi kawai ya ke bukatar tunawa idan aka kidima shi da tambaya a majalisar dokoki.

Wadannan kalmomi, a cewarsa, su ne “ba zan so in yi magana a kan daidaikun shari'o'i ba”, ko kuma “muna daukar mataki a kan batun kamar yadda doka ta tanada”.

'Yan adawa dai sun ce wannan magana cin fuska ce ga majalisar kuma suna shirin gabatar da shawarar daukar matakan ladabtarwa a kansa.

'Yan siyasa a kasar Japan sun sha fadawa cikin matsala sakamakon yin maganganun da ba su dace ba, ciki har da wani ministan yawon shakatawa, wanda ya yi murabus kwanaki hudu kacal bayan ya hau mukamin nasa, saboda cewar da ya yi mutanen Japan ba sa kaunar baki.

Murabus din Mista Yanagida dai ya zowa Firayim Minista Naoto Kan a wani mawuyacin lokaci da kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna goyon bayan da ya ke samu a tsakanin al'ummar kasar ya ragu matuka saboda yadda ya tafiyar da wata takaddama da kasar Sin, wato China.