Majalisun jihohin Najeriya sun kammala duba tsarin mulki

Majalisar dokokin Najeriya
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Kungiyar majalisun jihohin Najeriya ta mikawa majalisun dokokin tarayya kundin tsarin mulkin da aka aika mata, domin neman amincewar majalisun.

Majalisun jihohin sun amince da yawancin sauye-sauyen da majalisar dokokin tarayyar ta aika masu.

To amma akwai wasu sassa da basu amince da su ba.

Ana bukatar amincewar kashi biyu cikin uku na daukacin majalisun dokoki talatin da shidda na Najeriyar, kafin matakin yayi tasiri.