CDS ta zabi Mahaman Usman ya yi takara

Dan takarar C D S Mahaman Usman
Image caption An ta ja-in-ja kafin a tsaida Alhaji Mahaman Usman

A jamhuriyar Nijar, Jam'iyyar CDS Rahama ta tsayar da Alhaji Mahaman Usman a matsayin dan takararta na neman kujerar shugaban kasar a zaben da za a gudanar a watan Janairun badi.

Zaben Alhaji Mahaman Usman din dai ya biyo bayan janyewar Alhaji Abdu Labo, mataimakin shugaban jam'iyyar, a wani taro na musamman da uwar jam'iyyar ta kammala a daren jiya.

Alhaji Abdu Labo ya ce ya janye ya barwa Mahaman Usman ne bayan ya gindaya masa wadansu sharudda.

“Mun san Allah na son [jam’iyyarmu], amma na cewa [Alhaji Mahaman Usman] ya kamata bayan wannan [taro] a fitar da kudi a taimakawa [‘yan takararmu], a fitar da kudi a je a nemo ’yan majalisa.

“Na kuma cewa [Shugaba]: ‘wasu abubuwa da kake yi ka daina su—kana zuwa kana komowa ba da saninmu ba (mu ne kuma ke rike da jam’iyya) ba ka kiran babban sakatare, ba ka kira mataimakin shugaba’”.

Alhaji Mahaman Usman din dai ya yi godiya ga abokin takarar tasa, yana mai cewa wannan al’amari abin alfahari ne ga ‘yan jam’iyyar.

Ja-in-ja tsakanin ‘yan takarar biyu dai sai da ta kai ga kafa wani kwamitin sasantawa wanda bayan doguwar tattaunawa ya samu kaiwa ga wannan sakamako.

Karin bayani