Ana fatan gano mahaka ma'adinai da ransu

Daya daga cikin wuraren hakar ma'adinai a New Zealand
Image caption Daya daga cikin wuraren hakar ma'adinai a New Zealand

Ma'aikatan ceto a kasar New Zealand sun ce suna fatan gano mutanen nan ashirin da tara masu hakar ma’adinai da ransu.

Mutanen dai sun bace ne tun ranar Juma'ar da ta gabata bayan fashewar wani abu a mahakar ma'adinan da suke aiki.

Jami'in 'yan sanda mai kula da ayyukan ceto, Gary Knowles, ya ce ana shirin tura wani mutum-mutumi a cikin kogo don dauko hotuna da kuma tantance yanayin iskar da ke cikin mahakar.

“Za mu yi amfani da mutum-mutumi don samun damar shiga ciki har zuwa motar da muka tabbatar cewa tana cikin kogon”, inji jami’n.