Wani Jirgin soji yayi hatsari a Kamaru

Taswirar kasar Kamaru
Image caption Wani jirgin sojin kasar Kamaru ya fadi

Wani jirgin sama mai saukar ungulu na soja dake dauke da babban hafsan sojan kasa na Kamaru yayi hatsari.

Ya zuwa yanzu dai an gano gawarwaki hudu, yayin da ake cigaba da neman daya gawar da ta rage.

Daga cikin wadanda ke cikin jirgin har da wani dan kasar Isra'ila mai suna, Avi Sivan.

Shi dai Mista Sivan shi ne mai baiwa Shugaba Paul Biya shawara ta fuskar tsaro, kuma shi yake jagorantar rundunar nan ta samar da tsaro a yankin Bakassi mai arzkin mai.