INEC ta fitar da jadawalin zabe

Inec
Image caption Shugaban INEC Attahiru Jega tare da kwamishinonin sa

Hukumar zaben Najeria INEC ta ce ranar tara ga watan Apirilu na shekara ta 2011 ne za'a gudanar da zaben shugaban kasar.

Matakin da hukumar zaben ta dauka ya biyo bayan sauye-sauyen da aka aiwatar ne ga kundin tsarin mulkin kasar, lamarin da ya bada damar sauya lokacin zaben daga watan Janairu.

Hukumar zaben ta kasa INEC ce dai ta nemi a dage zaben ne, domin ta samu isasshen lokacin gudanar da zaben da ta ce, zai zamo karbabbe ga jama'a.

Tsayar da wa'adin ya kawo karshen rade-radin da ake ta yi game da jadawalin zaben.

Mako guda gabanin zaben shugaban kasar ne za'a gudanar da zabukan majalisun dokoki.

Yanzu haka Shugaba Goodluck Jonathan zai fafata ne da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar a zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP mai mulki.

Ranakun zabe

Zaben fitar da gwani na jam'iyyu: 26 Nuwamba - 16 Janairu Rajistar masu kada kuri'a: Janairu 15 - 29 Zaben 'yan majalisun tarayya: April 2 Zaben shugaban kasa: April 9 Zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi: April 16

Ra'ayin 'yan siyasa

To ko yaya 'yan siyasa ke kallon sabon jadawalin zaben da aka fitar? Injiniya Buba Galadima, dan kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa ta CPC, ya shaida wa BBC cewa abin ya zo musu da bazata.

"Ba mu zaci abin zai zo da sauri haka ba, a yanzu kokarin da muke yi shi ne na shirya zabukan jam'iyya, amma za mu yi iya yin mu domin ganin cewa mun cika wadannan sharuda".

Ya kara da cewa tun da dai doka ce to babu yadda za su yi, domin su masu kira ne da a bi doka, don haka za su mutunta wannan tsari.

A baya zabubbuka a Najeriya sun sha suka daga masu sa ido na gida da kuma kasashen waje, bisa zargin magudi da kuma satar kuri'u. Sai dai shugabannin Hukumar zaben na yanzu sun sha alwashin kawo sauyi da kuma gudanar da zaben da zai zamo karbabbe ga jama'a.