Gwamnatin Ireland za ta rage gibin kasafin kudin kasar

Masu Zanga Zanga a Ireland
Image caption Masu Zanga Zanga a Ireland

Gwamnatin Ireland ta bayyana wani gagarumin shiri na rage yawan kudaden da take kashewa domin rage yawan gibin kasafin kudin kasar.

A karkashin shirin gwamnatin ta na shirin rage gibin kasafin kudin da kimanin dalar Amruka biliyan ashirin a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Wannan shiri ya kunshi rage yawan kudaden da gwamnati take kashewa ne ta fuskar jin dadin jama'a, da biyan albashi na ma'aikatan gwamnati da kudaden fansho da kuma kara yawan kudaden haraji.

Gwamnatin Ireland ta dauki wannan mataki ne domin cika ka'idojin samun tallafi daga kasashen duniya wanda yawansa ya haura dala biliyan dari.

Firaministan Irelan, Brian Cowen, yace mutanen kasar suna da juriya sosai don hanka zasu iya shanye wannan kalubale.