Koriya ta Kudu ta bayyana yadda zata maida martani

Farmakin Koriya
Image caption Koriya ta kudu ta bayyana cewar irin martanin da zata mayar zai danganta ne da irin fasalin harin da koriya ta arewan ta kai mata

Koriya ta kudu ta bayyana irin yadda zata maida martani ga hari da makamai masu linzami da Koriya ta arewa ta kai ma ta

Harin da koriya ta arewan ta kaiwa koriya ta kudu dai yayi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla hudu, wadanda biyu daga cikinsu fararen hula ne.

Wani kakakin gwamnatin Koriya ta kudun yace, a baya dai suna kokarin kaucewa maida martani da karfin soja, amma yace daga yanzu, irin martanin da Koriya ta kudun zata maidawa Koriya ta arewan zai danganta ne ga irin fasalin harin da Koriya ta arewan ta kai masu.

Tuni dai Koriya ta arewa tayi gargadin cewa, zata kara kai wasu sabbin hare-hare idan har Korea ta kudu ta kara yin abinda ta kira tsokanar fada.