Za'a soma aikin gano gawarwakin mahakan New Zealand

Iyalan mahakan ma'adinan da suka mutu a New Zealand
Image caption Za'a soma bincike kan musabbabin fashewar abinda yayi sanadiyyar mutuwar mahakan ma'adinan kasar New Zealand su 29

Fira Ministan kasar New Zealand, John Key yace, za'a iya shafe watanni kafin a gano gawarwakin ma'aikatan hakar ma'adinan nan ashirin da tara da suka mutu sakamakon hatsarin da da ya shafi hako ma'adinai da kasar ba a taba ganin irinsa ba.

Fira Ministan ya kuma yi alkawarin gudanar da bincike dangane da musabbabin fashewar abinda ya kai ga hallaka ma'aikatan a karkashin kasa

John Key yace, dole a yiwa iyalan wadanda suka hallaka bayani akan abinda ya faru, sai dai kuma ya ce, za'a dau watanni kafin a samu cikakken bayani akan musabbbabin aukuwar lamarin.