Yan kasuwa a Niger sun katse safara ta Cotonou

Yan kasuwar Niger sun dakatar da safara ta Cotono
Image caption Yan kasuwar Niger sun dakatar da safara ta Cotono

A jamhuriyar Niger gidauniyar yan kasuwar kasar wato Chambre de Commerce ta yi kira ga yan kasuwar kasar masu shigo da kaya daga mashigin ruwan birnin COTONOU a jamhuriyar Bene da su kauracewa wannan hanya.

Hadadiyar kungiyar yan kasuwar Niger din ta dauki wannan mataki ne bayanda gwamnatin kasar Bene ta kara haraji akan wasu kayyayakin masarufi da suka hada da sukari, shinkafa da tufafffi.

Kungiyar ta yi zargin cewa wannan sabon haraji ya sabawa yarjejeniyar da kasashen biyu suka rattaba hannu a kai karkashin kungiyar kasashen ECOWAS ko CEDEAO.

Yarjenjeniyar dai ta kayyade yawan kudaden haraji da kasashen kungiyar za ta sanyawa kayayyakinda ake safararsu tsakanin kasashen kungiyar.