Sojojin ruwan Nijeriya sun kama dan Amruka da makamai

Rundunar sojojin ruwan Nijeriya tace ta kama wani dan kasar Amurka da ta ce yana kokarin shigar da makamai cikin Nigeria.

Rundunar sojin ruwan ta ce Ba-Amurke yayi sojan gona ne domin shigar da makaman da ta cafke a tashar jiragen ruwa da ke Lagos.

Tun farko dai rundunar ta bayar da sanarwar cafke wasu mutane biyu da suka shigo da wasu kananan makamai cikin wata mota da aka yiwa fentin motar sojoji.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da jami'an tsaron Nijeriya suka cafke irin wadannan makamai.

'Yan Nigeria da dama na bayyana fargabar su game da wannan abu da ke neman zama ruwan dare, musamman ganin yadda zabe ke tunkarawo a kasar.