Wen Jiabao ya ja hankalin yankin Koriya

Yakin Koriya
Image caption Firimiyan kasar China Wen Jiabao yayi kira da bangarorin biyu da suyi taka tsan- tsan

A martanin farko daga wani babban jami'in gwamnatin China dangane da harin makamai masu linzami da Korea ta arewa ta kaiwa Korea ta kudu, Primiyan Chinan, Wen Jiabao yayi kira ga bangarorin biyu su yi taka tsan-tsan sosai.

Firimiyan na China dai bai dorawa kowanne bangare alhakin aukuwar lamarin ba

sai dai kuma yayi kiran da a koma kan teburin shawara tsakanin kasashen nan shida dake shiga tsakani dangane da shirin nukiliyar Korea ta Arewa.