Ministan Koriya ta Kudu yayi murabus

Kim Tae-young, tsohon ministan tsaron Koriya ta Kudu
Image caption Kim Tae-young, tsohon ministan tsaron Koriya ta Kudu

Ministan tsaron Korea ta Kudu, Kim Tae-young ya yi murabus, kwanaki biyu bayan da sojojin Korea ta Arewa suka yi luguden wuta a kan wani tsibiri, mallakin Korea ta Kudu.

Rahotanni sun ce tuni shugaba Lee Myung-bak ya amince da murabis din nasa.

Mr Kim ya fuskanci kakkausar suka saboda rashin daukar kwararan matakan maida martani ga harin da Korea ta Arewa ta kai.

Yanzu dai Korea ta Kudun ta ce za ta canza ka'idojinta na aikin soja, tare da kara yawan sojojinta dake tsibirin da aka kaiwa harin.

A halin da ake ciki kuma, China ta nuna matukar damuwa dangane da wani atisayen soja da aka shirya yi tsakanin Korea ta Kudu da Amurka a karshen mako.