Shugaban Nijar ya sa hannu a kan sabon kudin tsarin mulki

Wasu sojojin Nijar
Image caption Sojoji sun ce za mu mika mulki ga farar hula a badi

A jamhuriyar Nijar dazu ne shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar, Janar Salou Djibo ya yi wani jawabi ga al'ummar kasar ta rediyo da talabijin.

Shugaban ya tabo batutuwa da dama da suka hada da batun zabubuka masu zuwa inda ya jaddada batun wa'adin mulki biyu na shugaban kasa da aka yi tanadi a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Tun farko dai Janar Salou Djibo ya rattaba hannu a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, bayan da a jiya kotun tsarion mulkin kasar ta yi na'am da sakamakon zaben raba gardama ne ko referendum da aka gudanar a watan Oktoba

Kaddamar da sabon kundin tsarin mulkin dai wani babban mataki ne da gwamnatin mulkin sojan kasar ta cimma dangane da alkawarin da ta dauka na shirya zabubuka a cikin shekara guda,su kuma mika mulki ga sabuwar gwamnati ran 6 ga watan afrilu na 2011.