Stalin ke da alhakin kisan kare dangin Katyn

Hoton Joseph Stalin
Image caption Hoton Joseph Stalin

'Yan siyasar kasar Russia sun amince da wani kuduri, wanda ya dorawa tsohon shugaban mulkin kama karya na Soviet, Joseph Stalin, alhakin bada umurnin aiwatar da kisan kare dangin Katyn, inda dakarun Soviet suka bindige dubban jami'an sojan kasar Poland, wadanda suka kama a lokacin yakin duniya na biyu.

Tarayyar Soviet ta kwashe shekaru 50 tana ikirarin cewa, 'yan Nazi ne na kasar Jamus suka yi kashe-kashen, kamin ta yarda cewa laifin ta ne, a 1990.

Kakakin majalisar dokokin Poland yayi marhabun da matakin da Rashar ta dauka

Ya ce zai taimaka wajen kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu, kamin ziyarar da shugaba Dmitry Medvedev zai kai a Poland a watan gobe.