China na kokarin sasanta rikicin Koriya

Kasar China ta zage damtse a kokarinta na samar da maslahar diflomasiyya a game da halinda ake ciki a yankin Korea, bayanda Korea ta Arewa ta ce, atisayen da kasashen Korea ta Kudu da Amurka ke shirin yi a karshen wannan mako ka iya kai yankin fadawa cikin yaki.

Wani dan kungiyar farar hula ta Royal United Services Institute, wato Alexander Neill ya ce girke jiragen yakin Amurka a yankin ka iya haifar da zullumi.

Ya ce wannan sabon salo da Amurka ta dauka na girke jiragen yakinta a tekun Yellow Sea, wanda ke kusa da yankinda ake takaddama a kai, zai iya matukar dagula alamura tare da rikita batun a cikin karshen mako.