Makomar kwalejojin ilimi a Nijeriya.

Taswirar Nijeriya
Image caption Taswirar Nijeriya

Wani al'amari da ke ci wa mutane da dama tuwo a kwarya a Nigeria, shi ne batun tabarbarewar harkokin ilimi, inda al'amarin a yanzu ya sa mutane da dama ke tura 'ya'yansu zuwa kasashen waje domin samun ilimi mai inganci, duk kuwa da irin dumbin asarar da hakan ke haddasawa ga Nijeriya.

Wata babbar matsala da mutane da dama ke ganin ta haifar da irin wannan al'amari shi ne irin rikon sakainar kashin da wasu gwamnatocin baya a Nijeriya suka yiwa harkar ilimi, musamman ma a lokacin mulkin soji.

Abun da ya sa mutane da dama suka kauracewa aikin Malanta. Wannan al'amari ya haifar da karancin kwararrun malamai, musamman a makarantun Piramare inda nan ne tushe.

Daga cikin sauye-sauyen da aka yi a 'yan shekarun baya domin tabbatar da samun kwararrun Malamai a irin wadannan makarantu, shi ne na tabbattar da cewa duk wanda zai koyar, yana da akalla takardar shaidar cancanta zama Malamin Makaranta watau NCE.

Kwalelojin tarayyar da yanzu gwamnati ke yin nazarin yi musu garambawul na daga cikin inda ake samun irin wannan takarda ta zama malamin makaranta.

Daga cikin bakinda muka gayyato sun hada da Malam Mohd Bala Abdu, wani kwararre akan harkokin ilimi, wanda ya koyar a makarantun, Piramare, da Sakandare da ma kuma Jami'a.

Akwai kuma Comrade Muhamad Auwal Ibrahim, Shugaban Kungiyar Malaman Makarantun Kwalejojin horad da Malamai.

Sannan akwai Honourable Alhaji Faruk Lawan, Shugaban kwamitin kula da harkokin ilimi a Majalissar wakilan Nigeria.

Sai kuma Comrade Muhammad Sani Uwaisu Zaria, Shugaban kungiyar Manyan Ma'aikatan Kwalejojin horad da malamai na kasa.