Ana zargin shugabankasar Kamaru da sayan kadara a Turai

Wani mabaraci a Kamaru
Image caption Ana zargin shugabankasar Kamaru da mallakar kadarori a kasar Faransa abinda mai magana da yawunsa yace babu gaskiya a ciki

Wani kakakin shugaban kasar Kamaru, Paul Biya ya musanta rahotannin da dake cewa, shugaban kasar ya mallaki gidaje a kasar Faransa.

Kakakin shugaba Paul Biyan, mai suna Martin Belinta Eboutou ya kuma ce, shugaban Kamarun ba shi da wata kaddara a Faransa ko kuma wata kasar waje.

Fadar shugaban Kamarun ta fitar da wannan sanarwa ne dai bayan wasu 'yan kasar Kamarun sun bayyana cewa, shugaba Paul Biya ya sayi wasu gidaje a kasar Farasansa.