Amurka ta yi gargadi kan fitar da bayanan sirri

Admiral Mike Mullen
Image caption Mike Mullen ya yi gargadi kan bayanan Wikileaks

Babban hafsan sojin Amurka, Admiral Mike Mullen ya ce, rayuka da dama za su shiga hatsari idan shafin Intanet, mai bankado asirai Wikileaks, ya aiwatar da aniyarsa ta wallafa bayanan sirri na gwamnatin Amurka.

Admiral Mullen ya ce dakarun Amurka da mutanen da suka yi aiki da su na iya fuskantar hare-haren daukar fansa.

Ana hasashen cewa bayanan sun shafi dangantakar Amurka ta hakika ne da gwamnatocin kasashen waje da shugabanninsu.

Sakatariyar hulda da kasashen waje ta Amurka ta zanta da wasu daga cikin wadanda ake hasashen za'a ambatosu cikin bayanan, a wani kokarin na karya lagon tasirin da ake jin wallafar za ta yi.