Yau za a rantsar da Aregbesola

Mista Rauf Aregbesola
Image caption Yau za a rantsar da Rauf Aregbesola

Idan an jima a yau ne za'a rantsar da sabon gwamnan jihar Osun a Najeriya, Mista Rauf Aregbesola.

A jawabinsa na farko, Aregbesola, wanda dan jam'iyyar adawa ta ACN ne, zai yi alkawarin kawo sauyi kan yadda ake gudanar da zabe a kasar, da mulkin kama-karya, da zalunci, kamar dai yadda daftarin jawabin na sa ya nuna.

A jiya Juma'a ne dai kotu ta tabbatar masa da mukamin bayan da ta hukunta cewa shi ne ya yi nasara a zaben gwamnan da aka gudanar a shekarar 2007.

Kotun ta ce Olagunsoye Oyinlola na jam'iyyar PDP ba shi ne zababben gwamnan jihar ba.

A watan jiya ma dai kotun ta soke zaben wani gwamnan na jam'iyyar PDP a jihar Ekiti.

'PDP tana juyayi'

Jam'iyar PDP ta ce soke zaben jihar Osun wani abin takaici ne.

Farfesa rufa'i Alkali, shi ne sakataren yada labaran jam'iyar na kasa, ya shaidawa BBC cewa: ''Wannan (soke zaben), gaskiya akwai takaici a ciki, akwai cin rai.Amma tunda ya ke mun yi alkawari a matsayinmu na babbar jam'iya ta kasa, muna kira ga mambobinmu na Osun, da sauran jihohin da abin ya shafa, su kara hakuri''.