Kotu ta daure 'yan Brotherhood a Misra

Shugaba Hosni Mubarak na Misra
Image caption Shugaba Hosni Mubarak na Misra

Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu a kan wadansu magoya bayan kungiyar nan ta ’Yan Uwa Musulmi (wato Muslim Brotherhood).

An dai tsare daruruwan ma'aikata wadanda ke adawa da gwamnatin kasar, gabanin zaben 'yan majalisun da za a gudanar gobe Lahadi.

Jami'ai sun ce an samu wadansu mutane goma sha biyu masu tsattsauran ra'ayi da laifin amfani da kalmomi na addini wajen neman magoya baya ga kungiyar, wacce tuni aka haramta ta a kasar.

Kungiyar ta Muslim Brotherhood, wacce 'ya'yanta ke takara ba a inuwar wata jam'iyya ba, ta bayyana hukuncin kotun a matsayin wani yunkurin mahukunta na neman muzgunawa 'yan adawa a kasar.

A nata bangaren, gwamnatin kasar ta yi alkawarin gudanar da zaben 'yan majalisun cikin adalci; sai dai kungiyoyin da ke kare hakkin bil'Adama sun ce tuni wasu dokoki masu tsauri suka yi tarnaki ga zaben.