Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Ireland

Masu zanga-zanga a Ireland
Image caption Masu zanga-zanga a Ireland

Dubban mutane ne dai suka jurewa sanyin dusar kankarar da ta lullube titunan birnin na Dublin suka fita don nuna rashin amincewa da matakan gwamnatin kasar Ireland na tsuke bakin aljihu.

Masu zanga-zangar dai sun ce wannan dan ba suka saka a jerin matakan nuna rashin amincewa da shirin gwamnatin na kara yawan kudin haraji, da kuma rage kudaden da take kashewa.

Shugabannin kungiyoyin kwadago dai sun zargi gwamnatin da kaddamar da yaki a kan talakawa, suna masu cewa gwamnatin za ta kashe makudan kudade wajen ceto bankunan kasar.

Wani mai magana da yawun kungiyoyin kwadagon, Macdara Doyle, ya shaidawa BBC cewa suna yin zanga-zangar ne don nunawa gwamnatin cewa kungiyoyin al'umma a kasar ba sa goyon bayan shirin nata.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu duk wani mataki da gwamnatin ta dauka na magance matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta bai haifar da komai ba sai koma-baya.

Kungiyoyin kwadagon sun kuma ce shirin zai jawo mutane dubu casa'in su rasa ayyukansu.