An hana zirga-zirgar motocin haya a Borno

Wani ofishin 'yan sanda da ake zargin 'yan Boko Haram da konawa
Image caption An hana zirga-zirgar motocin haya a Borno

Gwamnatin jihar Borno da ke arewacin Najeriya, ta kafa dokar hana zirga-zirgar motocin haya daga misalin karfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce an kafa dokar ne saboda sabon salon da 'yan bindigar da ake zargi da kashe mutane suka bullo da shi na amfani da kananan motocin haya wajen kaddamar da hare-hare kan mutane.

Sai dai jama'a da dama sun koka kan dokar, inda suka ce wata hanya ce ta takura musu a harkokin su na yau da kullum

A baya dai gwamnatin jihar ta hana amfani da baburan haya sakamakon zargin da ta yi cewa 'yan kungiyar Boko Haram, na amfani da su wajen kai hare-hare kan jama'a.