'Yan sanda sun karbe iko a Rio de Janeiro

'Yan sandan Brazil sun ce sun karbe iko daga yankunan dake kan tsauni na daya daga cikin unguwannin marasa galihu da aka fi yawan samun tashin hankali a birnin Rio de Janeiro, inda aka yi wa wasu dillalan miyagun kwayoyi kofar rago na tsawon kwanaki.

Sojoji da 'yan sanda da yawansu ya haura dubu biyu ne, da jiragen yaki masu saukar angulu, da kuma motoci masu sulke, suka fara kai sumame a unguwar ta Alemao a birnin na Rio da sanyin safiya.

An rika jin amon musayar wuta da manyan bindigogi.

Hukumomi sun ce akwai bukatar su raba wannan unguwa mai cike da jama'a da dillalan miyagun kwayoyi masu dauke da mugayen makamai.