An rufe rumfunan zabe a Ivory Coast

An rufe rumfunan zaben a Ivory Coast, a zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Tun da farko masu kada kuri'a sun kafa dogayen layuka a mazabu.

Shugaba Laurent Gbagbo mai ci shi ne yake fafatawa da tsohon praministan kasar, Alassane Ouattara, a zaben da ake cewar sakamakonsa zai kasance dab-da-dab.

Wani abun da ya dushe armashin yakin neman zaben shi ne tashin hankalin da aka yi jiya, da kuma dokar hana fitar dare da shugaban ya kafa.

Bayan kada kuri'arsa Mr Ouattara ya ce akwai yuwuwar sassauta dokar.

Ya ce, ina farin cikin cewa, bayan ganawarmu jiya, shugaban kasa ya amince da a dage wannan doka a yau.

Kuma za a kirga kuri'u cikin tsanaki.

Mutane akalla uku ne aka kashe a Abidjan, cibiyar kasuwancin kasar, a zanga zangar adawa da dokar.