'Shafin kwarmata bayanai na ta'addanci ne'

Tambarin shafin intanet na Wikileaks
Image caption Dan majalisa na son bayyana Wikileaks a matsayin na ta'addanci

Wani dan majalisar dokokin Amurka ya bukaci a dauki shafin intanet mai bankada asirai a matsayin kungiyar ta'addanci, bayan da shafin ya wallafa bayanan sirri na harkokin difilomasiyyar Amurka.

Peter King, wanda wakili ne a kwamitin tsaron kasa na majalisar wakilai ya ce, shafin na Wikileaks na jefa rayuwar Amurkawa da abokan huldarsu cikin hatsari.

Wallafa bayanan dai ya jawowa Amurka abin kunya saboda ya nuna yadda ta ke muzanta kawayenta, da kuma abokan gabanta.

Jaridu biyar ne dai a kasashe biyar suka wallafa wadansu daga cikin bayanan.