EFCC ta gayyaci wasu Manyan Jami'ai

Farida Waziri

Hukumar da ke ya ki da yiwa tattalin arziki zagon kasa a Nigeria EFCC, ta gayyaci kamfanin Halliburton da Manajan daraktan kamfanin SHELL da kuma wasu kamfanoni ukku da su bayyana a gabanta.

Goron gayyatar ya zo ne bisa zargin samun hannunsu ga abin kunyan nan na bayar da cin hanci daya tasamma dala miliyon 180 da kuma dola miliyon 240.

An yi zargin an bayar da wannan cin hanci ne a lokutta daban daban ga jami'an gwamnatin Naijeriya.

Hukumar EFCC ta saki mutanen da ta kama a makon jiya a kamfanin Halliburton na Nigeria wadanda suka hada da yan Nigeria da kuma kasashen waje. Amma Hukumar ta ce kada su kuskura su bar kasar har sai ta kammala bincikenta.